Isa ga babban shafi
Wasanni

Neymar ya sake jin rauni a idon sawunsa

Nishadin fafata wasan gasar Ligue 1 a ranar Lahadi tsakanin PSG da Saint-Etienne ya karewa Neymar cikin bazata, bayan da ya ji rauni a idon sawunsa lokacin da ya yi taho mu gama da daya daga cikin abokan karawarsa.

Jami'an lafiya, yayin fitar da Neymar daga filin wasan da PSG ke fafatawa da kungiyar Saint-Etienne.
Jami'an lafiya, yayin fitar da Neymar daga filin wasan da PSG ke fafatawa da kungiyar Saint-Etienne. © AP /Laurent Cipriani
Talla

Raunin dai sai da ya tilasta jami’an lafiya taimakawa Neymar wajen fiye daga cikin fili yana kuka.

Koda yake har yanzu ba a tabbatar da munin raunin ba, bayanan farko da aka tantance ya haifar da fargabar mai yiwuwa Neymar ya fama inda ya saba jin rauni ne a idon sawunsa, abinda ya sanya a shekarun baya ya taba share fiye da watanni 4 yana jinya.

Tun zuwansa PSG dai kaso mafi yawa na raunin da Neymar ke samu a idon sawunsa ne, zalika a kafa guda.

A karshen makon dai PSG ce ta lallasa Saint-Etienne da kwallaye 3-1, inda Lionel Messi taka muhimmiyar rawa wajen samun nasarar ciki har da taimakawa da yayi wajen zura kwallaye biyu daga cikin ukun da suka ci. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.