Isa ga babban shafi
Wasanni-Kwallon Kafa

Messi ya lashe Ballon d'Or a karo na bakwai

Lionel Messi ya lashe kyautar Ballon d’Or da ake bai wa gwarzon dan wasan kwallon kafa da ya fi nuna bajinta a shekara, inda ya doke abokan takararsa Robert Lewandowski da Karim Banzema wajen lashe kyautar.

Lionel Messi a wurin bikin lashe kyautar Ballon d'Or a birnin Paris na Faransa
Lionel Messi a wurin bikin lashe kyautar Ballon d'Or a birnin Paris na Faransa © FRANCK FIFE AFP
Talla

A karo na bakwai kenan da Messi ke lashe Ballon d’Or, yayin da yake ganin cewa, nasarar lashe wa kasarsa ta Argentina gasar kofin Kudancin Amurka, ita ce, ta sanya aka mika masa kyautar a bana.

An dai gudanar da bikin bada kyautar ce a Paris, birnin da ya bayyana a matsayin gida a gare shi jim kadan da komawarsa PSG don ci gaba da murza tamola bayan ya raba gari da Barcelona a cikin watan Agusta.

Masana harkar tamola a duniya sun bayyana cewa, babu wanda ya cancaci lashe Ballon d’Or a bara sama da Lewandowski, na Bayern Munich amma aka soke bikin bada ita saboda annobar Korona.

A bana dai, Lewandowski ne ya zo na biyu a jerin wadanda suka fi iya taka leda, sai Jorginho na Chelsea da ya yi na uku, yayin da Benzema na Real Madrid ya yi na hudu.

‘Yan jarida 180 ne daga sassan duniya ke zaman tantance dan wasan da ya cancaci lashe kyautar ta Ballon d’Or a duk shekara.

A bangaren mata kuwa, yar wasan Barcelona Alexia Putellas ce ta lashe kyautar ta Ballon d’Or a wannan shekara ta 2021.

Putellas mai shekaru 27 ta taimaka wa Barcelona wajen lashe gasar cin kofin zakarun Turai ta mata , yayin da ta kafa tarihin zama ‘yar wasan tsakiya mafi zurara kwallaye a nahiyar Turai bangaren mata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.