Isa ga babban shafi
Wasanni-Kwallon Kafa

Klopp na fatan Liverpool ta huce takaicin da Everton ta kunsa mata

Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Liverpool Jurgen Klopp ya yi fatan tawagarsa ta yi ramuwar gayya yayin haduwarsu da Everton yau laraba karkashin gasar firimiyar Ingila, don huce haushin illar da ta yi mata a kakar da ta gabata.

Manajan kungiyar kwallon kafa ta Liverpool Jurgen Klopp.
Manajan kungiyar kwallon kafa ta Liverpool Jurgen Klopp. Paul ELLIS AFP
Talla

Wasan wanda ke matsayin na dabi tsakanin kungiyoyin biyu da ke gari guda, wannan ne karon farko cikin kusan kaka uku da zai gudana a filin wasa na Goodison Park tare da halartar magoya bayan kowanne bangare.

Watanni 13 da suka gabata ne Virgil van Dijk ya gamu rauni yayin wata haduwarsa da mai tsaron ragar Everton Jordan Pickford yayin wasan kungiyoyin biyu, wanda ya tilastawa mai tsaron bayan karkare ilahirin kakar yana jinya.

Ka zalika watanni bayan hakan Thiago Alcantara ya sake samun rauni duk dai a haduwar Liverpool din da Everton wanda shima ya tilasta masa jinyar watanni.

Liverpool dai na ganin raunin masu tsaron bayan nata a Goodison Park ne ya haddasa mata koma baya a kakar da ta gabata, ta yadda ta gaza kare kambunta na firimiya ko da ya ke tasha da kyar wajen iya karkare kakar a matsayin ta 3 a teburi.

Acewar Jurgen Klopp fatansa shi ne Liverpool ta mayar da hankali wajen fanshe illar da Everton ta yi mata kamar yadda magoya baya ke bukata.

Duk da cewa Liverpool na nuna bajinta a wannan kaka, amma koda yaushe haduwarta da Everton na zame mata kalubale dai dai lokacin da yanzu haka ta ke matsayin ta 3 tazarar maki 2 tsakaninta da Chelsea jagora.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.