Isa ga babban shafi
Wasanni

Tsohon shugaban hukumar IAAF Lamine Diack ya rasu yana da shekaru 88

Tsohon shugaban hukumar Wasannin Tsalle-tsalle da Guje-guje ta Duniya, Lamine Diack ya rasu ya na da shekaru 88 a rayuwarsa kamar yadda iyalansa suka tabbatar wa Kamfanin Dillancin Labarai na AFP.

Tsohon shugaban hukumar kula da gasar guje-guje da tsalle-tsalle Lamine Diack,dan asalin kasar Senegal.
Tsohon shugaban hukumar kula da gasar guje-guje da tsalle-tsalle Lamine Diack,dan asalin kasar Senegal. AFP/Archives
Talla

Marigayin dan asalin Senegal  ya jagoranci hukumar ta IAAF tsakanin shekarar 1999 zuwa 2015 kafin daga bisani a tuhume shi da laifin cin hanci da rashawa.

Wata kotun Faransa ce ta same shi da aikata laifi a shekarar 2020  bayan an zarge shi da karbar miliyoyin kudade domin yin rufa-rufa game da ‘yan wasan Rasha masu kwankwadar miyagun kwayoyi.

A wancan lokaci, an zartar masa da hukuncin zaman gidan kaso na tsawon shekaru hudu, amma daga bisani aka soke shekaru biyu tare da cin sa tarar Dala dubu 560.

Marigayin ya taba zama kusa a Hukumar Wasannin Olympics ta Duniya tsakanin 1999 zuwa 2013.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.