Zan dawo da martabar Barcelona - Hernandez
Kocin Barcelona Xavi Hernandez ya lashi takobin dawo da martabar kungiyar a matakin kololuwa a nahiyar Turai, bayan da Bayern Munich ta fitar da su daga gasar cin kofin zakarun Turai, inda ta lallasa su da ci 3-0.
Wallafawa ranar:
A karon farko kenan cikin shekaru 21 da ake yin waje da Barcelona a matakin rukuni a gasar ta zakarun Turai.
Tun kakar shekara ta 2003-04, Barcelona ke kaiwa matakin kuniyoyi 16 a gasar, amma a wannan karon al’amarin ya sauya.
Kocin na Barcelona ya ce, yana cikin fushi, kuma ba ya jin dadin abin da ke faruwa da kungiyar a yanzu, yayin da ya kara da cewa, daga yanzu za su bude sabon babi na daga darajar kungiyar wadda ta lashe kofin zakarun Turai sau biyar.
Ko a wasansu zagaye na farko a Camp Nou a cikin watan Satumba, sai da Bayern Munich ta yi wa Barcelona ci 3-0.
Tuni jaridun Sifaniya suka yi ta yi wa Barcelona raddi kan rashin tabuka abun kirki, inda jaridar AS ta bayyana ficewar Barelonar a matsayin murabus din kungiyar daga kwallon kafa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu