Isa ga babban shafi
Wasanni-Kwallon Kafa

Karuwar masu covid-19 ya sa Firimiya tunanin dage wasu wasanni

Hukumar gudanarwar Firimiya ta ce har zuwa yanzu ba ta tsayar da magana kan bukatar kungiyoyin kwallo suka shigar mata ba, game da neman dage musu wasanninsu zuwa nan da sabuwar shekara ta 2022, saboda tsanantar masu harbuwa da covid-19 musamman sabon nau'in Omicron.

Fiye da 'yan wasan Firimiya 50 ne yanzu haka suka harbu da cutar ta covid-19 tun bayan bullar nau'in Omicron.
Fiye da 'yan wasan Firimiya 50 ne yanzu haka suka harbu da cutar ta covid-19 tun bayan bullar nau'in Omicron. Glyn KIRK AFP/File
Talla

Manajojin Firimiya da dama sun shigarwa hukumar gudanarwar gasar bukatar ganin an sauya lokutan wasanninsu na karshen disamba zuwa karshen makon farko na sabuwar shekara wato ranakun 8 da 9 ga watan na Janairu, kenan dai dai da lokacin da za a yi zagaye na 3 na wasannin gasar cin kofin FA.

Bisa tanade-tanaden Firimiya dai wasanni za su dawo ne a ranar 15 ga watan Janairu, sai dai bukatar kungiyoyin na nuna cewa wadanda abin ya shafa baza su yi amfani da kwarya-kwaryan hutun lokacin ba.

Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ta ce ta samu karin 'yan wasa 3 da suka harbu da sabon nau’in corona na Omicron sai dai duk da haka kungiyar ta ce wasanta da Everton zai tafi kamar yadda aka tsara.

Manaja Thomas Tuchel wanda bai bayyana sunan karin ‘yan wasan 3 da suka harbu da cutar ba, ya ce za a killace dukkanin wadanda suka yi cudanya da su, alkaluman da suka zama kari kan dan wasan tsakiyar Croatia Matteo Kovacic da ke killace yanzu haka bayan harbuwa da cutar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.