Isa ga babban shafi
Wasanni-Kwallon Kafa

Sai mun gudanar da gasar Afrika - Shugaban CAF

Shugaban Hukumar Kwallon Kafa ta Afirka CAF, Patrice Motsepe, ya ce gasar cin kofin kasashen nahiyar ta AFCON za ta gudana kamar yadda aka tsara a kasar Kamaru, daga ranar 9 ga watan Janairu.

Shugaban CAF, Dr. Patrice Motsepe
Shugaban CAF, Dr. Patrice Motsepe © CafOnline Media
Talla

Sanarwar da Motsepe ya bayar na zuwa ne a daidai lokacin da shakku ke kara yin karfi dangane da makomar gasar cin kofin kasasshen nahiyar ta Afirka, saboda wasu dalilai, daga hada da  rashin jituwa tsakanin kungiyoyin kwallon kafar kasashen Turai, musamman na Ingila da kuma hukumomin kwallon kafar kasashen Afirka kan sakin manyan ‘yan wasansu domin wakiltar kasashen su a gasar ta AFCON.

Wani karin dalilin da ke neman zama barazana ga gudanar gasar kofin na kasashen Afirka,  shi ne batun yaduwar annobar Korona, cutar da ke neman sake barkewa a wani sabon zango, tun bayan gano sabon nau’inta mai suna Omicron da kwararru suka yi ittifakin ya zarce sauran nau’ikan annobar saurin yaduwa.

Wannan na zuwa ne bayan shugaban Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya FIFA Gianni Infantino, ya bayyana cewa tawagarsa na tattaunawa da Hukumar Kwallon Kafar Afirka CAF da kuma sauran masu ruwa da tsaki wajen shirya gasar cin kofin Afrikar a shekarar 2021, domin ganin ko za a iya dage gasar zuwa watan Satumba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.