Isa ga babban shafi
Wasanni

Gasar Firimiya: 'Yan wasa da maikata 103 sun kamu da Korona

Hukumar kula da gasar Premier ta ce ‘yan wasa da ma’aikatanta 103 sun kamu da cutar Korona a tsakanin 20 zuwa 26 ga Disamba.

Daya daga cikin filayen wasannin da kungiyoyi kwallon kafa ke fafatawa cikinsu a gasar Firimiya.
Daya daga cikin filayen wasannin da kungiyoyi kwallon kafa ke fafatawa cikinsu a gasar Firimiya. AFP/Archives
Talla

Sanarwar da hukumar gasar Firimiyar ta fitar ta ce an gano ‘yan awsa da ma’aikata fiye da 100 da suka kamu da Koronar ce, dafa cikin adadin mutane dubu 15 da 186 da aka yi wa gwajin kamuwa da cutar.

Kawo yanzu dai an dakatar da wasanni 15 na gasar Firimiya a cikin watan Disamba nan, yayin da aka dage wasanni uku da ke kasa da matakin farko na gasar ta Firimiya.

Daga wasannin da aka soke akwai karawa tsakanin Liverpool da Leeds, sai Watford da Wolves da kuma wanda za a kara tsakanin Burnley da Everton.

Zalika an dakatar da wasan da Arsenal za ta kara da Wolves a ranar Talata, bayan da a ranar Lahadi aka samu karuwar adadin masu Korona cikin 'yan wasan Wolves.

Sai dai duk da karuwar masu Korona a tsakanin ‘yan wasa, kungiyoyin da ke buga gasar Firimiya sun yi watsi da shawarar dakatar da kakar wasan da ake ciki zuwa wani lokaci a nan gaba, don dakile yaduwar cutar tsakanin ‘yan wasan.

Kungiyoyin dai sun tsaya kan cewa matukar kowacce daga cikinsu na da ‘yan wasa 13 lafiyayyu da kuma mai tsaron raga, to wasanni za su ci gaba da tafiya kamar yadda aka tsara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.