Isa ga babban shafi
Wasanni

Cutar Korona ta kutsa cikin sansanin 'yan wasan Algeria

Yan wasan Algeria da suka hada da Youcef Belaili, da Mohamed Amine da Hussein Benayada suka kamu da cutar, yayin da ake gaf da fara gasar cin kofin kasashen Afirka, nan da mako guda.

'Yan wasan kasar Algeria
'Yan wasan kasar Algeria REUTERS/Amr Abdallah Dalsh
Talla

Mai horas da tawagar kwallon kafar kasar Algeria, Jameel Belmadi ne ya shaidawa wani taron manema labarai halin da ake ciki a birnin Doha, inda ‘yan wasan na Algeria ke gudanar da atisaye kafin tashi zuwa Kamaru domin fafatawa a gasar AFCON.

Koci Belmadi ya ce dan wasan gaba Yusuf Belaili zai iya komawa atisaye nan da kwanaki biyu masu zuwa, amma 'yan wasa masu tsaron baya da suka hada da Mohd Ameen da Hussaini Benayada a halin yanzu suna Algeria, kuma za su shiga cikin tawagar kasar ne nan da kwanaki masu dan dama.

Algeria mai rike da kofin gasar cin kofin kasashen Afirka za ta kara da Saliyo da Equatorial Guinea da kuma Ivory Coast a wasannin matakin rukuni.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.