Isa ga babban shafi
Wasanni-Kwallon Kafa

'Yan fashi sun raunata Joao Cancelo na Manchester City

Mai tsaron baya na Manchester City Joao Cancelo ya samu rauni a wani farmaki da ‘yan fashi suka kai gidansa da ke arewacin London a daren jiya alhamis.

Mai tsaron baya na Manchester City Joao Cancelo.
Mai tsaron baya na Manchester City Joao Cancelo. REUTERS - CRAIG BROUGH
Talla

Cancelo dan Portugal mai shekaru 27 ya wallafa hotonsa a shafinsa na Instagram wanda ke nuna raunin da ya samu a fuska, inda ya ce ‘yan fashin su hudu sun yi kokarin cutar da iyalinsa dalilin da ya sanya shi rikici da su har ya kai ga sun ji masa ciwo.

Acewar mai tsaron bayan na City ‘yan fashin sun kwace sarkokinsa na zinare dana iyalinsa amma basu cutar da iyalin nasa ba face ciwon da suka ji masa a fuska.

Acewar Cancelo raunin ko kuma fargabar abin da ya faru a lokacin fashin ba zai karya masa gwiwa wajen bayar da gudunmawar da ta kamata a karawar kungiyarsa ta gobe asabar tsakaninta da Arsenal karkashin firimiyar Ingila ba.

Daga Juventus ne Manchester City ta sayo Cancelo cikin watan Agustan 2019 yayinda yanzu haka yak e matsayin ‘yan wasan da ke taka rawar gani a cikin tawagar ta Pep Guardiola wadda ke matsayin jagorar teburin firimiya da tazarar maki 8 tsakaninta da mai biye mata Chelsea.

Tuni dai Manchester City ta fitar da sanarwar da ke tir da farmakin kan mai tsaron bayan nata tare da nuna goyon baya gareshi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.