Isa ga babban shafi
Wasanni-Kwallon Kafa

Liverpool ta kulle sansanin atisayen 'yan wasanta saboda covid-19

Kungiyar kwallon kafa ta Liverpool ta kulle sansanin atisayen ‘yan wasanta biyo bayan karuwar masu harbuwa da covid-19 ciki har da mataimakin manaja Pep Lijnders da gwaji ya tabbatar ya harbu a yau, matakin da ya tilasta dage wasan kungiyar da Arsenal karkashin gasar cin kofin kalubale ko kuma Carabao a gobe alhamis.

Mataimakin manajan Liverpool Pepijn Lijnders da ya jagoranci wasan kungiyar a karawarta da Chelsea.
Mataimakin manajan Liverpool Pepijn Lijnders da ya jagoranci wasan kungiyar a karawarta da Chelsea. Adrian DENNIS AFP/File
Talla

Sanarwar da kungiyar ta wallafa a shafinta ta ce ta rufe sansanin na AXA da ke Melwood ne don dakile ci gaba da yaduwar cutar ta covid-19 tsakanin ‘yan wasanta.

Kafin harbuwar Lijnders dai, dama ‘yan wasan Liverpool irinsu mai tsaron raga Alisson Becker da Joel Matip da Roberto Firmino baya ga uwa uba kocin tawagar tuni suka killace kansu bayan harbuwa da covid-19.

Harbuwar Lijnders, wanda ya jagoranci Liverpool a karawarsu da Chelsea da suka yi canjaras 2 da 2 na nuna kungiyar ba ta da zabin da ya wuce dakatar da wasanta zuwa wani lokaci.

Baya ga ‘yan wasan da suka harbu da cutar Liverpool na fuskantar karancin ‘yan wasa yanzu haka irinsu Thiago Alcantara da Takumi Minamino da Divock Origi wadanda dukkaninsu ke fama da rauni sai kuma irinsu Mohamed Salah da Sadio Mane da Naby Keita wadanda suka tafi wakiltar kasashensu a gasar cin kofin Afrika.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.