Isa ga babban shafi
Wasanni-Kwallon kafa

Aston Villa na zawarcin Philippe Coutinho daga Barcelona

Kungiyar kwallon kafa ta Aston Villa na harin Philippe Coutinho na Barcelona a wannan kasuwar musayar ‘yan wasan dai dai lokacin da dan wasan mai shekaru 29 ke fatan raba gari da kungiyar ta Catalonia.

Philippe Coutinho na Barcelona da ya shafe shekara guda a Bayern Munich matsayin aro.
Philippe Coutinho na Barcelona da ya shafe shekara guda a Bayern Munich matsayin aro. AFP/File
Talla

Barca da kanta na son rabuwa da dan wasan  bayan sayo Ferran Torres daga Manchester City kan yuro miliyan 55.

Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Aston Villa Steven Gerard wanda ya taka leda tare da Coutinho dan Brazil a Liverpool na fatan kawo dan wasan don cirewa kungiyar kitse a wuta.

Baya ga Aston Villa da ke harin Coutinho akwai kungiyoyi irinsu Arsenal da Everton da Newcastle United da Tottenham dukkaninsu na firimiya da ke shirin sayen danw asan a wannan lokaci, haka zalika ana alakanta shi da tsohuwar kungiyar Liverpool.

Coutinho na fatan farfado da kansa ne tun bayan fuskantar gagarumar koma baya a fagen tamaula lokacin da Barca ta saye shi kan yuro miliyan 142 daga Liverpool a 2018.

Zamansa a Barcelona ya kassara karsashin danw asan wanda ya shafe kakar wasa guda a Bayern Munich matsayin aro haka zalika ya kasa samun damar taka leda yadda ya kamata da kungiyar.

Steven Gerard wanda yam aye gurbin Dean Smith a Aston villa yayin jawabinsa kan matakin fara tuntubar Coutinho ya ce yana da yakinin dan wasan zai taimaka wajen daga likkafar kungiyar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.