Isa ga babban shafi
Wasanni

Pogba na shirin zama dan wasa mafi albashi a tarihin gasar Firimiya

Hukumar gudanarwar Manchester United ta yi wa Paul Pogba tayin biyansa fan 500,000 duk mako domin shawo kan dan wasan na Faransa ya ci gaba da zama a kungiyar.

Paul Pogba
Paul Pogba PETER CZIBORRA POOL/AFP/File
Talla

Idan har Pogba ya amince da sabon albashin, zai kafa tarihin zama dan wasa mafi yawan albashi a gasar Firimiyar Ingila.

Sabon tsarin albashin da aka gabatarwa Pogba ya zarce abin da tauraron kulob din na United Cristiano Ronaldo ke samu duk mako.

Cristiano Ronaldo
Cristiano Ronaldo Janerik HENRIKSSON TT NEWS AGENCY/AFP/Archives

Bayan komawa United daga Juventus a bazarar da ta gabata, Cristiano Ronaldo ya zama wanda ya fi kowa karbar albashi a kungiyar inda ake biyansa fam dubu 400,000 a mako.

Yanzu haka dai Pogba na cikin watanni shida na karshe a yarjejeniyarsa da Manchester United bayan da ya ki amincewa da tattaunawa kan tsawaita zamansa a kungiyar.

Kungiyoyin Real Madrid da Paris Saint-Germain da Juventus ne kungiyoyin da ke kan gaba a Turai wajen fatan sayen dan wasan na Faransa kafin ko kuma a lokacin sabuwar kakar wasanni.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.