Isa ga babban shafi
Wasanni

Real Madrid ta kai wasan karshe na Super Cup bayan doke Barcelona da kyar

Real Madrid ta samu nasarar kaiwa wasan karshe na gasar Super Cup bayan doke abokiyar hamayyar ta Barcelona da kwallaye 3-2 yayin fafatawar da suka yi a daren ranar Laraba a kasar Saudiya.

'Yan wasan Real Madrid yayin murnar kaiwa wasan karshe na gasar Super Cup, bayan doke Barcelona da 3-2, yayin wasan da suka fafata a Saudiya.
'Yan wasan Real Madrid yayin murnar kaiwa wasan karshe na gasar Super Cup, bayan doke Barcelona da 3-2, yayin wasan da suka fafata a Saudiya. FAYEZ NURELDINE AFP
Talla

Madrid ta samu nasarar cin kwallayenta ne ta hannun ‘yan wasanta Vinicius Junior da Karim Benzema, da kuma Federico Valverde wanda jefa tasa a cikin mintuna 30 an karin lokaci, ita kuwa Barca ta samu nasata kwallayen ne ta hannun Ansu Fati da kuma Luuk de Jong.

A halin yanzu, Real Madrid za ta jira wanda za ta kara da shi a wasan karshe na gasar ta Super Cup ne, tsakanin ko dai Atletico Madrid ko kuma Atletic Bilbao, kungiyoyin da su kuma za su kara a daren yau Alhamis.

Sau 11 Real Madrid ta lashe kofin gasar Super Cup, yayin da Barcelona ke da kofin 13.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.