Isa ga babban shafi
Wasanni

United na tattaunawa da Pochettino a asirce

Batun zabin wanda Manchester United za ta kulla yarjejeniyar dindindin da shi a matsayin kocin ‘yan wasanta na cigaba da daukar hankali, inda bayanai suka ce har yanzu kocin PSG na yanzu wato Mauricio Pochettino ke kan gaba a tsakanin wadanda ake kyautata zaton za su karbi jagorancin horas da kungiyar ta United.

Mai horas da kungiyar PSG Mauricio Pochettino
Mai horas da kungiyar PSG Mauricio Pochettino FRANCK FIFE AFP/File
Talla

Jaridar ‘Le Parisien’ da ke Faransa ta ruwaito cewar tun bayan korar Ole Gunnar Solksjaer a cikin watan Nuwamban bara shugabannin Manchester United suke da aniyar kulla yarjejeniya da Pochettino, kuma har yanzu suna nan akan bakansu tare da cigaba da tuntubarsa.

A halin yanzu kwantiragin Pochettino da PSG zai kare ne a shekarar 2023, amma ga dukkanin alamu ba lallai ya kai lokacin ba, saboda wasu matsaloli da yake fama da su a kungiyar, ciki har da yiwuwar rasa damar lashe gasar cin kofin Zakarun Turai ta bana, inda cikin watan Fabarairu za su kara da Real Madrid a zagayen gasar na biyu da ya kunshi kungiyoyi 16.

Kocin rikon kwarya na Manchester United Ralf Rangnick
Kocin rikon kwarya na Manchester United Ralf Rangnick Paul ELLIS AFP/File

Sai dai rahotanni sun ce duk da cewar kocin na PSG na da magoya baya da dama a United, kocin kungiyar na yanzu da ke rikon kwarya Ralf Rangnick, wanda kuma shi ne babban mashawarcin kungiyar a nan gaba, ya fi son kulla yarjejeniya da Erik ten Hag kocin kungiyar Ajax.

Mutum na uku kuma da Manchester United din ka iya dauka don horas da ‘yan wasanta shi ne Brenden Rodgers kocin Leicester City.

Bayanai sun ce, idan har Pochettino ya koma Manchester United, PSG za ta yi karkata hankalinta ne wajen kulla yarjejeniya da tsohon kocin Real Madrid Zinadine Zidane.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.