Isa ga babban shafi
Wasanni-Kwallon Kafa

Lewandowski ya lashe kyautar gwarzon FIFA

Dan wasan Bayern Munich dan asalin Poland Robert Lewandowski ya lashe kyautar FIFA ta gwarzon dan wasan shekara bangaren maza.

Robert Lewandowski
Robert Lewandowski FRANCK FIFE AFP
Talla

A karo na biyu kenan a jere da Lewandowski mai shekaru 33 ke samun irin wannan kyauta  bayan ya zazzaga kwallaye har guda 69 a raga.

Ya doke Mohamed Salah na Liverpool da kuma Lionel Messi na PSG wajen lashe wannan kyauta ta Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya, FIFA.

Lewandowski ya gogo tarihin da Gerd Muller ya kafa shekaru 49 da suka gabata na zama dan wasan da ya fi zura kwallo a raga a gasar Bundesliga a cikin kalandar wasanni a shekara guda.

Lewandowski ya yi nasarar zura kwallaye guda 43 cikin wasanni 34 da ya buga a gasar ta Bundesliga.

A bangare guda, an karrama Cristiano Ronaldo na Manchester United a matsayinsa na dan wasa da ya fi zura kwallo a tarihi a matakin wasannin kasa da kasa bangaren maza, inda ya jefa kwallaye 115 a wasanni 184.

Kazalika, an ayyana kocin Chelsea, Thomas Tuchel a matsayin mai horasawa mafi nuna bajinta, ganin yadda ya jagoranci kungiyar ta Chelsea har zuwa matakin wasan karshe a gasar cin kofin zakarun Turai sau biyu, duk da cewa, a cikin watan Janairu ya karbi aikin horas da kungiyar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.