Isa ga babban shafi
Wasanni

Kasashe shida sun tsallaka zuwa zagayen kwata final a gasar AFCON

Zuwa yanzu kungiyoyi shida ne suka samu kaiwa zagayen kwata final a gasar cin kofin Afrika da Kamaru ke karbar bakunci.

'Yan wasan kasar Morocco, yayin murnar samun nasara kan takwarorinsu na Malawi da kwallaye 2-1.
'Yan wasan kasar Morocco, yayin murnar samun nasara kan takwarorinsu na Malawi da kwallaye 2-1. REUTERS - MOHAMED ABD EL GHANY
Talla

Senegal da Morocco ne  kasashe na baya-bayan nan da suka samu tsallakawa zagayen wasan na daf da na kusa da na karshe a jiya Talata.

Senegal ta lallasa Cape Verde ne da 2-0, yayin da Morocco ta doke Malawi da ci 2-1.

Tuni dai Tunisiya da Kamaru da Burkina Faso da kuma Gambia suka shiga zagayen nag aba, inda Tunisia za ta kara da Burkina Faso, mai masaukin baki Kamaru kuwa  za ta kara ne da Gambia a zagayen na kwata final.

A yau Laraba za a buga sauran wasannin zagayen da ya kunshi kasashe 16 na gasar ta cin kofin Afrika, inda Ivory Coast za ta kara da Masar, yayin da Mali za ta kara da Equatorial Guinea.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.