Isa ga babban shafi
Wasanni-Kwallon Kafa

An sake bai wa matan Iran damar shiga filin wasa don kallo

Hukumomi a Iran sun bai wa matan kasar damar kallon wasan kwallon kafa da aka fafata tsakanin tawagar kwallon kafar kasar da ta Iraqi a jiya Alhamis, inda Iran din suka samu nasara.

Matan Iran da suka shiga filin wasa don kallon wasan neman tikitin shiga gasar cin kofin duniya ta 2022  tsakanin kasarsu da Iraq.
Matan Iran da suka shiga filin wasa don kallon wasan neman tikitin shiga gasar cin kofin duniya ta 2022 tsakanin kasarsu da Iraq. ATTA KENARE AFP
Talla

Wannan damar dai ta zo ne a karon farko cikin kusan shekaru 3.

Jamhuriyar musulinci ta Iran ta haramta wa mata shiga filayen wasanni don yin kallo tsawon shekaru 40.

Manyan malaman Musulinci da aka dauki wannan matakin da su sun yi ittifakin cewa dole ne a hana mata shiga muhallin da maza ne ke mu’ammala a cikin suturar da bata rufe wasu sassan jikinsu ba.

A watan Satumban shekarar 2019 hukumar kula da kwallon kafa ta duniya ta umurci Iran ta bari mata su shiga kallon wasa a filayen wasa, lamarin da ya sa mata suka yi cincirindo zuwa filayen wasanni  bayan Iran ta bada wannan dama a lokacin.

A karon farko tun wancan lokaci, an kebe tikitin shiga kallon wasan neman shiga gasar cin kofin duniya da aka gwabza tsakanin Iran da Iraq guda 2,000 daga cikin dubu 10 wa  mata.

Tun bayan juyin juye hali na Irana shekarar 1979, mata ne suka fi jin zafin dokokin sauye sauye da aka bijiro da su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.