Isa ga babban shafi
WASANNI - afcon

Senegal ta lashe gasar kofin kwallon kafar Afirka ta farko

Ƙasar Senegal ta lashe gasar cin kofin ƙwallon ƙafar Afirka ta farko a tarihinta, bayan nasarar doke Masar da ci 4 -2 a bugun finareti a wasan karshe da aka doka a filin wasa na Olembe dake Yaounde babban birnin kasar Kamaru, bayan shafe shekaru 60 tana jira.

Tawagar kwallon kafar Senegal lokacin da suke murnar lashe gasar cin kofin Afirka ta Kamaru ta karbi bakwanci bayan doke Masar da ci 4 -2 a bugun Finareti. 06/02/2022.
Tawagar kwallon kafar Senegal lokacin da suke murnar lashe gasar cin kofin Afirka ta Kamaru ta karbi bakwanci bayan doke Masar da ci 4 -2 a bugun Finareti. 06/02/2022. CHARLY TRIBALLEAU AFP
Talla

Sadio Mane da ya barar da bugun finareti a mintuna na shida na soma wasa, har sai da aka shafe mintuna 120 ana fafatawa ba tare da an samu wanda ya ci a fili ba, har sai da aka kai bugun daga kai sai mai tsaron gida Manen ya fitta kisa a wuta bayan da ‘yan wasan Masar biyu suka barar da bugun na daga kai sai mai tsaron raga.

Dan wasan tawagar kwallon kafar Senegal lokacin da suke murnar lashe gasar cin kofin Afirka ta Kamaru ta karbi bakwanci bayan doke Masar da ci 4 -2 a bugun Finareti. 06/02/2022.
Dan wasan tawagar kwallon kafar Senegal lokacin da suke murnar lashe gasar cin kofin Afirka ta Kamaru ta karbi bakwanci bayan doke Masar da ci 4 -2 a bugun Finareti. 06/02/2022. Kenzo TRIBOUILLARD AFP

Karo na biyu kenan da tawagar Lion Teranga na kasar Senegal ke zuwa wasan karshe na cin kofin Afirka ba tare da nasara ba, sai a wannan karo, yayin da Masar ta barar da damar daukar kofin a karo na 8, wanda da zai kasance na farko da Mohammed Salah.

Dan wasan Senegal Sadio Mane da abokin wasan sa na Masar Mohamed Salah tare da mai tsaron bayan na Masar Gabaski yayin wasan karshe na cin kofin Afirka a Kamaru, 06/02/22
Dan wasan Senegal Sadio Mane da abokin wasan sa na Masar Mohamed Salah tare da mai tsaron bayan na Masar Gabaski yayin wasan karshe na cin kofin Afirka a Kamaru, 06/02/22 © FMM / Pierre René-Worms

'Yan wasan da suka nuna bajinta

Dan wasan tawagar indomitable Lion na Kamaru masu masaukin baki da suka tsari da tagulla a mataki na uku, Vincent Abubakar shine dan wasan da yafi zura kwallo a gasar, da kwallaye takwas kuma ya karbi takalmin zinare.

Dan wasan tawagar kwallon kafar Kamaru Vincent Aboubacar,
Dan wasan tawagar kwallon kafar Kamaru Vincent Aboubacar, © AFP

Sai kuma mai tsaron bayan Senegal da Chelsea Edouard Mendy, ya zama golan da yafi takwarorinsa a gasar.

Dan wasan Senegal da Liverpool, Sadio Mané ya lashe kyautar gwarzon dan wasan da yafi kowa a gasar.

Sai kuma golan Masar Mohamed Abou Gabal ‘Gabaski’ shi ne ya zama gwarzon dan wasan karshe na gasar AFCON.

Paul Biya

Shugaban kasar Paul Biya mai shekaru 88 a duniya, ya halarci bikin rufe taron inda aka yi masa faretin a cikin wata budaddiyar mota gaban dumbin jama'a tare da uwargidansa, Chantal Biya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.