Zakarun Turai: Benzema na fatan fafatawa a wasan Madrid da PSG
Karim Benzema yana da yakinin cewa zai samu kuzarin da zai fafata a wasan kungiyarsa, Real Madrid da Paris Saint-Germain a wasan gasar zakarun nahiyar Turai in an jima a Talatar nan, bayan da ya yi jinyar rauni a kafarsa.
Wallafawa ranar:
A jiya Litinin dan wasan gaban na Real Madrid ya shaida wa manema labarai cewa ya ji garau, kuma yana jin cewa za a iya damawa da shi.
Benzema, wanda shine dan wasan da ya fi kowa saka kwallaye a raga a Real Madrid, inda ya ci kwallaye 24 a dukkan gasa, bai buga wa kungiyar tasa wasanni 3 ba tun bayan da ya fita daga fili yana dingishi a wasan da suka barje gumi da Elche 2-2 a ranar 23 ga watan Janairu.
Benzema ya ce fafatawarsa da kylian Mbappe a bangaren PSG wani abu ne na musamman a gareshi, duba da yadda ake ta rade radin zai koma Madrid, da kuma ganin cewa dukkanninsu su na yi wa tawagar Faransa wasa.
Bangarorin 2 za su hadu ne a filin wasa na Parc des Princes, kana su yi fafatawa ta 2 a Madrid ranar 9 ga watan Maris.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu