Isa ga babban shafi
Wasanni-Kwallon Kafa

Arsenal, Barcelona na neman Alvaro Morata

Har yanzu Arsenal da Barcelona na sha’awar dauko dan wasan gaba nan, Alvaro Morata a karshen wannan kaka, kamar yadda jaridun labarin wasanni da dama suka ruwaito , ciki har da Calciomercato.

Alvaro Morata dan wasan da Arsenal da Barcelona ke nema.
Alvaro Morata dan wasan da Arsenal da Barcelona ke nema. Vincenzo PINTO AFP
Talla

A halin da ake ciki, Alvaro Morata mai shekaru 29 yana wasa a matsayin aro a Juventus, sai dai tun bayan da ta sayo Dusan Vlahovic a watan Janairu, ana ta rade radin dan wasan zai koma ainihin kungiyarsa, wato Atletico Madrid.

Hakan ne ma ya sa Arsenal da Barceloa ke ta fafutukar ganin sun dauko dan wasan, amma kuma babbu wata magana mai karfi ya zuwa yanzu.

Sai dai har yanzu kungiyoyin biyu na dakon ganin ya koma ainihin kungiyarsa din a Spain a karshen wannan kaka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.