Isa ga babban shafi
UEFA- RASHA

Uefa zata dauke wasan karshe na gasar zakarun Turai daga St Petersburg

Hukumar shirya wasannin kwallon kafar Turai Uefa na Shirin sauya wasan karshe na gasar cin kofin zakarun Turai na bana daga St Petersburg saboda rikicin Ukraine da Rasha.

Logo da kofin gasar zakatrun Turai.
Logo da kofin gasar zakatrun Turai. OZAN KOSE AFP
Talla

Yanzu haka Rasha ta aike da dakaru zuwa yankuna biyu dake karkashin ikon 'yan tawaye a gabashin Ukraine kuma ana fargabar cewa ana shirin kai hari.

Kasashe da dama, ciki har da Birtaniya, sun gabatar da takunkumi kan Rasha a matsayin martani kan matakin.

Don haka ne hukumar ke da tabbacin zai yi wuya ta yi yunƙurin daukar bakuncin wasan a Rasha.

Tsohuwar ministar wasanni ta Burtaniya Tracey Crouch ta shaida wa manema labarai cewa ya kamata Uefa ta yi gaggawar janye wasan karshen daga Rasha.

Za'a tantance

Ko da yake Hukumar kula da kwallon kafa ta nahiyar turai tace tana tantance halin da ake ciki a Rasha kafin daukar mataki, amma ta shirya tsaf domin neman wani sabon wuri cikin kankanin lokaci don doka wasan karshen karo na uku tun bayan barkewar annobar korona.

Shekaru biyu da suka gabata dai a kasar a kasar Portugal aka buga wasan karshe na gasar cin kofin zakarun Turai saboda barkewar annobar Covid-19.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.