Isa ga babban shafi
Wasanni-Kwallon Kafa

FIFA da UEFA sun haramtawa kungiyoyin Rasha doka wasanni saboda Ukraine

FIFA da UEFA sun sanar da dakatar da duk wasu kungiyoyin kwallon kafar Rasha gami da tawagar kwallon kafar kasar daga kowacce gasa saboda yakin da kasar ke yi yanzu haka da Ukraine.

Shugaba Vladimir Putin tare da shugaban hukumar FIFA Gianni Infantino yayin gasar cin kofin duniya da Rasha ta dauki nauyi a 2018.
Shugaba Vladimir Putin tare da shugaban hukumar FIFA Gianni Infantino yayin gasar cin kofin duniya da Rasha ta dauki nauyi a 2018. AFP - ALEXEY NIKOLSKY
Talla

Sanarwar da UEFA ta fitar ta ce kungiyoyin za su fice daga duk wata gasa da suke ciki har zuwa abin da hali zai yi.

Wannan mataki na UEFA nan una cewa tawagar kwallon kafar Rasha ta maza baza ta doka wasannin na suka rage mata na neman gurbi a gasar cin kofin duniya ba, haka zalika tawagar mata baza ta ci gaba da wasannin cin kofin euro ba.

Hukuncin na UEFA ya shafi hatta kungiyar Spartak Moscow wadda ke matakin kwata final a gasar Europa wanda zai taimakawa abokiyar karawarta RB Leipzig tsallake matsakin cikin sauki.

Bugu da kari EUFA ta dakatar da daukar nauyin kamfanin makamashi na Rasha Gazprom.

Cikin wata sanarwar hadin gwiwa da FIFA da UEFA suka fitar, sun ce duniyar kwallo a hade take kuma suna tare da al’ummar Ukraine a wannan gaba.

Kafin tattaunawar kusoshin hukumomin biyu dai, a jiya FIFA ta sahalewa tawagar Rasha ta doka wasanninta amma ba tare da tuta ko taken kasa ba, amma wasu kasashen Turai suka yi tirjiya kan matakin.

Sai dai hukumar wasannin Rasha ta yi watsi da hukuncin hukumomin biyu tare da shan alwashin daukaka kara a kotun wasanni don neman adalci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.