Isa ga babban shafi
Wasanni

Manchester City ta lallasa United da kwallaye 4-1

Kwallayen da Kevin De Bruyne da kuma Riyad Mahrez suka ci, na daga cikin adadin kwallaye 4 da suka baiwa Manchester City damar lallasa Manchester United da ci 4-1 a gasar Firimiya.

'Yan wasan Manchester City yayin murnar lallasa Manchester United da kwallaye 4-1.
'Yan wasan Manchester City yayin murnar lallasa Manchester United da kwallaye 4-1. © Getty Images
Talla

Rashin nasarar ta United ta nuna cewar a halin yanzu akwai tazarar maki 22 tsakaninta da City a gasar Firimiya bayan fafatawar da suka yi a wannan Lahadin.

Har wa yau kayen da Manchester United ta sha yana barazanar dakile damarta kan kokarin halartar gasar zakarun Turai a kakar wasa mai zuwa.

Yanzu haka dai kungiyar ta Red Devils ta koma ta 5, biye da Arsenal da maki daya wadda ke matsayi na hudu, wadda ita ma take da kwantan wasanni uku da bata buga ba.

Liverpool ma da ke matsayin ta biyu a bayan Manchester City, tana da kwantan wasa 1 da bata buga ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.