Isa ga babban shafi
Wasanni-Kwallon Kafa

Lashe kofin La Liga ba zai gagara ba-Xavi

Lashe gasar La Liga abu ne mai yiwuwa ga Barcelona a cewar mai horar da ‘yan wasan kungiyar Xavi Hernandez.

Xavi Hernandez, kocin Barcelona.
Xavi Hernandez, kocin Barcelona. AFP/Archives
Talla

Barcelona dai ta yunkuro bayan da ta samu koma baya, inda yanzu ta lashe wasanni 4, bayan da ‘yan wasan da ta cefano a watan Janairu suka kara mata karsashi.

Har yanzu dai saura maki 7 su cimma wadda ke matsayi na 2, kuma yaran na  Xavi Hernandez suna da kwanten wasa 1 a hannu, tare kuma da gwabazawar da za su yi da Camp Nou.

Wannan ne abin da y aba Xavi kwarin gwiwa har ya sa da aka tambaye shi ko za su iya lashe gasar La Liga ya amsa da cewa ‘abu ne mai yiwuwa’.

Sai dai abu ne mai wuya Real Madrid ta rikito duk da maki 15 da take jan ragamar gasar da shi ana saura wasanni 11 a karkare La Liga.

xavi ya ce idan lissafi za a yi,  Barcelona na iya lashe La Liga, sai dai matsalar ita ce kowa na rashin nasara a gasar a halin yanzu amma ban da Real Madrid.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.