Isa ga babban shafi
Wasanni-Kwallon Kafa

Italy da Argentina za su kara da juna a Wembley yayin wasan Finalissima

UEFA ta sanar da filin wasa na Wembley da ke birnin London a matsayin wajen da za a doka wasa tsakanin zakarar Turai Italiya da zakarar America wato Argentina mai rike da kambun Copa America.

Tawagar kwallon kafar Italiya lokacin da ta yi nasarar lashe kofin Euro bayan doke Ingila a bugun fenariti.
Tawagar kwallon kafar Italiya lokacin da ta yi nasarar lashe kofin Euro bayan doke Ingila a bugun fenariti. Pool via REUTERS - MICHAEL REGAN
Talla

Karawar wadda za ta gudana ranar 1 ga watan Yuni mai zuwa, Italy ta samu zarafin kaiwa matakin ne bayan doke Ingila a wasan karshe na EURO cikin watan Yulin bara a bugun fenariti yayinda a bangare guda Argentina ta iya kaiwa matakin bayan itama ta lallasa Brazil da kwallo 1 mai ban haushi.

A watan Satumban bara ne hukumomin CONMEBOL da na UEFA suka tattauna tare da dawo da kwarya-kwaryar gasar da aka yi wa lakabi da ‘‘Finalissima’’ da aka tsara za ta rika gudana tsakanin zakarun nahiyoyi gabanin tabbatar da ita a watan Disamban bara, yayinda kuma UEFA ta sanar  rana da kuma lokacin gudana da ita a jiya talata.

Tawagar Argentina bayan doke Brazil a wasan karshe na cin kofin Copa America.
Tawagar Argentina bayan doke Brazil a wasan karshe na cin kofin Copa America. © REUTERS - Amanda Perobelli

Sanarwar da UEFA ta fitar ta ce sabuwar gasar tsakanin zakarun nahiyoyin biyu zai baiwa ‘yan kallo damar kallon zakarun biyu a fili guda suna fafatawa.

Ita dai wannan gasa dama akan gudanar da ita tsakanin zakarun nahiyoyin biyu amma aka dakatar da gudanar da ita tun daga shekarar 1993.

Irin wannan haduwa ta karshe da aka gudanar ita ce haduwar Argentina da Denmark a wancan lokaci inda tawagar Argentina karkashin jagorancin Diego Maradona ta lallasa Denmark.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.