Benzema ya sake cin kwallaye 3 cikin wasa 1 a gasar Zakarun Turai
Kwallayen da Karim Benzema ya ci wa Real Madrid ya basu damar doke Chelsea da kwallaye 3-1, nasarar da ta sanya masu rike da kofin gasar zakarun Turai shiga tsaka mai wuyar ficewa daga gasar zakarun Turai a matakin Kwata Final.
Wallafawa ranar:
Benzema ne dai ya jefa dukkanin kwallaye ukun a ragar Chelsea, inda ya ci biyu kafin tafiya hutun rabin lokaci, ta uku kuma bayan dawowa daga hutun zangon farko na karawar da suka yi.
A bangaren Chelsea, Kai Havertz ne ya rage tazarar da aka samu da kwallo 1 tilo da ya ci wa kungiyar ta sa.
Wani abu da ya dauki hankali yayin wasan dais hi ne yadda golan Chelsea Edouard Mendy ya yi kuskuren da ya baiwa Benzema damar jefa kwallo ta uku a ragarsu.
Wannan ne karo na biyu da Benzema ya ci kwallaye uku cikin wasa guda wato Hat-trick a turance, cikin gasar cin kofin zakarun Turai, bayan da shi kadai ya ci kwallayen uku a karawarsu da Paris Saint-Germain a wasa na biyu na zagayen da ya kunshi kungiyoyi a gasar Zakarun Turai.
Sai a ranar 12 ga watan Afrilun nan Chelsea za ta yi tattaki zuwa birnin Madrid domin sake karawa da abokiyar hamayyar ta a karo na biyu.
Kofin gasar zakarun Turai na karshe da Real Madrid ta lashe shi ne na 13 a shekarar 2018.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu