Isa ga babban shafi

Za a yi gwanjon rigar Maradona kan fam miliyan 4

Rigar da Diego Maradona ya saka a lokacin da ya zura kwallo a ragar Ingila ta hanyar amfani hannunsa a gasar cin kofin duniya ta shekarar 1986, ana sa ran za a sayar da ita a kan akalla fam miliyan 4.

Rigar da Maradona ya sanya a wasan da suka samu nasara kan Ingila, yayin gasar cin kofin duniya ta shekarar 1986.
Rigar da Maradona ya sanya a wasan da suka samu nasara kan Ingila, yayin gasar cin kofin duniya ta shekarar 1986. © AFP Photo/Sotheby's
Talla

Rigar dai a yanzu mallakin tsohon dan wasan tsakiya ce na Ingila Steve Hodge, wanda ya yi musayar riga da Maradona bayan da Argentina ta doke su da ci 2-1.

A kimanin shekaru biyu da suka gabata, bayan mutuwar Maradona a 2020, Hodge ya ce rigar gwarzon dan wasan ba ta siyarwa ba ce.

Diego Maradona yayin murnar lashe gasar cin kofin duniya bayan lallasa West Germany da kwallaye 3-2 a shekarar 1986.
Diego Maradona yayin murnar lashe gasar cin kofin duniya bayan lallasa West Germany da kwallaye 3-2 a shekarar 1986. AP - Carlo Fumagalli

Maradona, wanda ya jagoranci Argentina zuwa nasarar lashe gasar cin kofin duniya a 1986, na daga cikin manyan gwarazan ‘yan wasa a tarihin kwallon kafa, ya mutu yana da shekaru 60 sakamakon bugun zuciya.

Rigar da gwarzon duniya na kasar Brazil Pele ya sanya a wasan karshe na gasar cin kofin duniya a shekarar 1970 ita ce rigar kwallon kafa mafi tsada da aka sayar da ita a gwanjo, a cewar littafin adana ababen tarihi na duniya wato ‘Guinness World Records’.

An gwanjon rigar ta Pele ce kan kudi fam miliyan 157 da dubu 750 a shekarar 2002.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.