Isa ga babban shafi

Klopp ya kamanta karawarsu da City da damben boxing

Har yanzu ana tafe kusan kana-kan-kan tsaknain Manchester City da Liverpool a Firimiyar Ingila, bayan da a jiya kungiyoyin da ke kan gaba a gasar suka tashi 2-2 a wasan da suka fafata a filin wasa na Etihad.

Mai horas da Liverpool Jurgen Klopp.
Mai horas da Liverpool Jurgen Klopp. APA/AFP
Talla

Sau biyu ne dai Manchester City da ke gida ta sha gaban Liverpool a yayin karawar ta jiya, sai dai bakin sun farke duka kwallayen ta hannun ‘yan wasansu Diogo Jota da Sadio Mane, yayin da City ta samu na ta daga hannun Kevin de Bruyne da kuma Gebrial Jesus.

Yayin da yake tsokaci bayan wasan kocin Liverpool Jurgen Klopp ya bayyana karawar da suka yi a jiya tamkar wasan damben boxing inda da zarar an kiba maka naushi kake mayar da martani kana samun dama.

Har yanzu dai Manchester City ke kan gaba a gasar Firimiya da maki 74, Liverpool biye da maki 73, sai Chelsea ta uku da maki 62.

A can kasan Teburi kuma Norwich ne da Watford masu maki 21 da 22.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.