Isa ga babban shafi
Wasanni

Mun sha kaskanci a hannun Liverpool - Kocin Man-U

Kocin rikon kwarya na Manchester United Ralf Rangnick ya bayyana lallasar da suka sha a hannun Liverpool a matsayin kaskanci.

Ralf Rangnick
Ralf Rangnick dpa/AFP/File
Talla

A jiya da daddare ne Liverpool ta yi kaca-kaca da  Manchester United da kwallaye 4-0 a filin wasa na Anfield a gasar firimiyar Ingila, abin da ya bai wa Liverpool damar darewa saman teburin gasar.

Tuni Manchester United ta sauko zuwa mataki na 6 a teburin wadda hakan babbar barazana ce a gare ta ta rashin samun gurbi a gasar zakarun Turai.

Manchester United ta yi wasan na jiya ba tare da Cristiano Ronaldo ba, wanda ke cikin jimamin mutuwar dansa, yayin da magoya bayan Liverpool da Manchester United suka yi tarayya wajen karrama dan nasa a minti bakwai da saka wasan na jiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.