Isa ga babban shafi
Wasanni-Kwallon Kafa

Ronaldo zai fafata a karawar Man United da Arsenal

Cristiano Ronaldo ya shirya tsaf don ffatawa. wasann da kungiyarsa Manchester United za ta gwabza da Arsenal a ranar Asabar a gasar Firimiyar Ingila, kwanaki bayan mutuwar jaririnsa.

Cristiano Ronaldo, dan wasan gaba na Manchester United.
Cristiano Ronaldo, dan wasan gaba na Manchester United. Pool via REUTERS - LASZLO BALOGH
Talla

Ronaldo bai taka leda ba a wasan da Liverpool ta lallasa kungiyarsa 4-0, amma ya dawo atisaye a ranar Laraba, kuma kocin wucin gadi Ralf Rangnick ya tabbatar da cewa dan wasan mai shekaru 37 zai kasance cikin tawagar da za ta yi tattaki zuwa Emirates.

Rangnick ya ce Scott McTominay zai dawo fagen fafatawa, duba da cewa ya yi atisaye, haka ma Rafael Varane. Bayan wadannan, in ji kocin, saura ‘ya wasan da suka ji rauni su na ci gaba da jinya.

Rabon United da lashe wasa a filin Anfield tun a watan Disamban shekarar 2017, kuma Rangnick yana fatan cewa ‘yan wasansa za su mayar da martini ga dukan da Liverpool suka yi musu a ranar Talata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.