AC Milan ta hau saman teburin Serie A bayan doke Lazio
AC Milan ta koma saman teburin gasar serie A ta kasar Italiya bayan da ta jefa wata kwallo a ragar Lazio a cikin mintunan karshe na wasan da suka fafata.
Wallafawa ranar:
Milan din sun yi sakaci har dan wasan Lazio Ciro Immobile ya saka musu kwallo a raga a cikin minti na 4 da fara wasa.
Bayan hutun rabin lokaci Olivier Giroud ya farke kwallon, inda bayan nan ne Milan suka ci gaba da matsa wa Lazio lamba har Zlatan ya kawo wata kwallo da Sandro Tonali ya ci.
Yanzu AC Milan sun bai wa Inter Milan tazarar maki 4 a saman teburin, da saura wasanni 4 a Karkare gasar, amma wasanni 3 suka rage wa AC Milan din.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu