Zakarun Turai: Za'a rubuta sabon tarihi tsakanin Madrid da City
Manchester City za ta karbi bakuncin Real Madrid a filin wasa na Etihad a yammacin wannan Talata a zagen farko na wasan kusa dana karshe na gasar cin kofin zakarun Turai. Zakarun gasar Premier sun casa Atletico Madrid a wasan daf da na kusa da na karshe a gasar, yayin da Real Madrid ta doke Chelsea kafin zuwa wannan matsayi na Semi-Final.
Wallafawa ranar:
Man City za ta yi kokarin amfani da damar samun nasara a wasan farko a gidanta kafin wasan da za a yi a gidan Madrid a ranar 4 ga watan Mayu, don zuwa wasan karshe da kungiyoyin ingila biyu ko kuma na Spain biyu zasu hadu a bana, yayin da Liverpool da Villarreal ke shirin fafatawa a wannan Laraba.
Tarihin haduwar kungiyoyin biyu
Sau shida Manchester City da Real Madrid suka hadu a baya, kuma kowa ya yi nasara sau biyu, yayin da sukayi canjaras sau biyu.
Haduwar Farko
Ganawarsu ta farko ta zo ne a matakin rukuni na gasar cin kofin zakarun Turai na shekarar 2012-13, inda Real Madrid ta ci 3-2 a Bernabeu kafin a raba maki a karawar da suka yi a Manchester watanni biyu bayan haka.
Haduwar ta biyu
Ƙungiyoyin biyu sun sake haduwa a wasan kusa da na karshe na gasar Champion League a 2015-16; karawar ta farko dai ta kare ne babu ci a filin wasa na Etihad kafin Los Blancos ta yi nasara a wasa na biyu da ci 1-0 a Bernabeu sakamakon kwallon da Fernando ya ci gida.
Haduwar karshe
Bangarorin biyu sunyi haduwar karshe a matakin zagaye na ‘yan 16 na gasar zakarun Turai a shekarar 2019-20; Man City ta yi nasara a karawar farko da ci 2-1 a Madrid ta kuma kara ci a gida da ci 2-1 a watan Agustan 2020, wanda ya bata jimillar kwallaye 4-2.
Madrid bata taba cin City a Etihad ba
Real Madrid bata taba nasara kan city a Etihad ba, wato filin wasanta na gida, inda ta ci daya kuma ta yi canjaras a wasanni biyun ukun da suka kara.
Gabaɗaya:
Man City - nasara sau biyu
Real Madrid - nasara sau biyu
Canjaras - sau biyu
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu