Isa ga babban shafi

An kama mutumin da ya yi fitsari a kan mutum-mutumin dan wasan Sunderland

An kama wani mai goyon bayan kungiyar Newcastle saboda yin fitsari akan wani mutum-mutumi na Bob Stokoe, tsohon koci kuma dan wasan Sunderland da ya kasance tauraronta a zamanin baya.

Mutum-mutumin Bob Stokoe, tsohon koci kuma dan wasan Sunderland da wani magoyin bayan Newcastle ya yiwa fitsari.
Mutum-mutumin Bob Stokoe, tsohon koci kuma dan wasan Sunderland da wani magoyin bayan Newcastle ya yiwa fitsari. © Sunderland Echo
Talla

A wata sanarwa da kakakin Sunderland ya fitar a ranar Litinin, ya ce tuni an mika wannan batu ga 'yan sanda, matakin da jami’an tsaron suka tabbatar, inda suka ce suna cigaba da gudanar da bincike.

Mutum-mutumin Stokoe yana wajen filin wasan kungiyar ne don tunawa da irin gudunmawar da ya baiwa kungiyar.

An kuma sassaka mutumutimin ne don nuna yadda tsohon manajan yake rawa a filin wasa, bayan nasarar da suka samu wajen doke Leeds United a wasan karshe na gasar cin kofin FA a shekarar 1973.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.