Isa ga babban shafi

Bournemouth ta koma gasar Firimiyar Ingila

Kungiyar Bournemouth ta samu gurbin komawa gasar Firimiyar Ingila, bayan da ta doke Nottingham Forest da ci 1-0 a gasar Championship da ke mataki na biyu a kasar ta Ingila.

Wasu daga cikin magoya bayan kungiyar Bournemouth, yayin murnar nasarar sake komawa buga gasar Firimiyar Ingila.
Wasu daga cikin magoya bayan kungiyar Bournemouth, yayin murnar nasarar sake komawa buga gasar Firimiyar Ingila. © Reuters/Matthew Childs
Talla

Nasarar dai ta sanya Bournemouth komawa kan matsayi na biyu a gasar ta Championship yayin da ya rage ta buga wasa daya, yayin da kuma tuni Fulham ta lashe gasar, abinda ya sanya tuni kungiyoyin biyu suka samu komawa gasar Firimiya bayan shafe shekaru biyu basa cikinta.

Ita kuwa kungiyar Nottingham Forest za ta buga wasa ne bai daya, wanda idan har ta samu nasara, za ta koma gasar Firimiyar, inda rabon da ta bayyana tun shekarar 1993, yau shekaru 29.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.