Abin kunya ne Barcelona ta kasa kulla yarjejeniya da Haaland - Xavi
Kocin Barcelona Xavi Hernandez ya koka kan kalubalen da kungiyarsa ke fuskanta a dangane da shirin kulla yarjejeniya da manyan ‘yan wasa, a daidai lokacin da kakar wasa ta bana ke shirin karewa, da kuma tsara fuskantar wadda ke tafe.
Wallafawa ranar:
Xavi ya bayyana haka ne, a lokacin da manema labarai suka bukaci tsokacinsa akan yarjejeniyar da kungiyar Manchester City ta kulla da Erling Haaland daga Borussia Dortmund a ranar Talata.
Kocin na Barcelona ya ce abin kunya ne a ce sun gaza yin gogayyar neman jan ra’ayin Haaland tsakaninsu da City, kamar yadda suka rasa damar kulla yarjejeniya da Dusan Vlahovic dan wasan da Juventus ta dauka a cikin watan janairun da ya gabata.
A cewar Xavi gaskiyar halin da Barcelona ke ciki shi ne kungiyar ba za ta iya kulla yarjejeniya da manyan ‘yan wasan da take fatan su taka mata leda ba, a kakar wasa mai zuwa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu