Isa ga babban shafi

Fofana ya lashe kyautar Mark Vivien Foe

Seko Fofana, ‘dan kasar Cote d’Ivoire ya lashe kyautar Dan wasan Afirka da yafi kowa fice a cikin gasar Lique 1 a kakar bana, wanda RFI da France 24 ke shiryawa kowacce shekara domin girmama tsohon ‘dan wasan Kamaru Mark Vivien Foe da ya mutu.

Seko Fofana.
Seko Fofana. © Photo AFP - Montage FMM
Talla

Fofana dake yiwa RC Lens wasa ya samu nasara ne akan Hamari Traore dan kasar Mali da Gael Kukuta dan kasar Congo da kuma Nayef Aguerd dan kasar Morocco.

An dai haifi Fofana ne a birnin Paris, kuma ya yiwa Faransa wasa a matsayin matashi, kafin daga bisani ya koma yiwa Cote d’Ivoire wasa a shekarar 2017.

Kyautar Marc Vivien Foe da aka yi wa lakabi da ‘dan wasan Kamaru da ya mutu ranar 26 ga watan Yunin shekarar 2003, ana bayar da ita ne ga ‘dan wasan da ya fito daga Afirka da ya yi fice a gasar Lique 1, kuma mutane 70 ke zabo wanda yake lashe kyautar da suka hada da ‘Yan Jaridu da tsoffin Yan wasa da kuma masu harkokin wasanni.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.