Isa ga babban shafi

Manchester City ta lashe gasar Premier League ta bana 2021/22

Manchester City ta lashe kofin gasar Premier na bana kuma na takwas a jumlace, bayan doke Aston Villa 3-2 a Etihad ranar Lahadi.

Manchester City ta lashe kofin gasar Premier na bana kuma na takwas a jumlace, bayan doke Aston Villa 3-2 a Etihad jiya Lahadi.
Manchester City ta lashe kofin gasar Premier na bana kuma na takwas a jumlace, bayan doke Aston Villa 3-2 a Etihad jiya Lahadi. © Manchester City
Talla

Aston Villa ta fara zura kwallaye biyu tun a zagayen farko ta hannun Matty Cash da Philippe Coutinho, amma bayan dawowa daga hutun rabin lokaci wasa ta sauya, cikin mintuna biyar City ta zura kwallao uku a ragar Villa, ta hannun Ilkay Gundogan wanda ya farke na farko a mintuna na 76, sai Rodrigo Hernandez, sannan Ilkay Gundogan ya kara na uku a minti na 81, wato kwallaye biyu kenan ya zura a karawar.

Manchester City ta lashe kofin gasar Premier na bana kuma na takwas a jumlace, bayan doke Aston Villa 3-2 a Etihad ranar Lahadi, 22/05/22.
Manchester City ta lashe kofin gasar Premier na bana kuma na takwas a jumlace, bayan doke Aston Villa 3-2 a Etihad ranar Lahadi, 22/05/22. © Manchester City

 

'Yan baiwa

Manajan kungiyar Pep Guardiola ya bayya ‘yan wasan City amatsayin ‘yan baiwa sakamakon lashe kofin na EPL 4 a kaka biyar.

City ta kammala gasar da maki 93 daya tsakaninta da liverpool mai biye mata da maki 92, Chelsea ke na uku da maki 74, sai Tottenham a matsayi na hudu da maki 71.

PSG

Tun kafin wannan lokaci Paris Sint Germain ta lashe Gasar Ligue 1 ta kasar Faransa, bayan da ta tashi 1-1 da RC Lens a wasan mako na 34 cikin watan Afrilu, yanzu haka ta karkare gasar da maki 86, yayin da Marseille ta zo na biyu da maki 71, sai monaco da maki 69 sannan Rennes da maki 66.

Mbappe

Tuni dan wasan PSG Kylian Mbappe ya watsawa Madrid kasa a ido bayan yanke shawarar ci gaba da zama a kungiyar dake taka leda a gasar Ligue 1.

 

Dan wasan PSG Kylian Mbappé
Dan wasan PSG Kylian Mbappé © AFP - ANNE-CHRISTINE POUJOULAT

 

 

Madrid

Itama Real Madrid ta lashe gasar La Liga karo na 35 tun kafin karkare gasar.

Madrid ta karkare kakar bana da maki 86, Barcelona ken a biyu na maki 73, sai Atletico ken a uku da maki 71 sai kuma Sevilla da maki 70 amatsayi na 4

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.