Isa ga babban shafi

Liverpool ta yi fatali da farashin Mane

Liverpool ta yi fatali da tayin da Bayern Munich ta yi na biyen Pam miliyan 30 a matsayin farashin sayen Sadio Mane.

Sadio Mane
Sadio Mane AFP/File
Talla

Rahotanni sun ce, Liverpool ta yi matukar mamaki da irin wannan tayin, inda aka ce abin da take so Bayern Munich ta ba ta a matsayin farashinsa ya kai Euro miluyan 50, kwatankwacin Pam miliyan 42.8 kenan.

Liverpool dai ta yi la’akari ne da yadda ita ma Bayern Munich ta kiyasta darajar dan wasanta Robert Lewandowski.

Shi ma Lewandowski na son komawa Barcelona bayan ya shafe tsawon shekaru 10 a kungiyar.

Mane da Lewandowski dukkaninsu na da shekara guda-guda da suka rage musu a kungiyoyinsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.