Liverpool ta sayi dan wasan Benfika Darwin Nunez kan yuro milyan 100
Benfika ta sanar da saida dan wasanta Darwin Nunez dan asalin Uruguay ga Kungiyar Liverpool kan kudi Yuro miliyan dari.
Wallafawa ranar:
Nunez mai shekaru 22, yajefa kwallaye 34 a wasa 41 daya dokawa Benfica a kakar data gabata
Harwa yau dan wasa shine ya jefawa ita kanta Liverpool din kwallo biyu a raga a haduwar su da Benfica a gasar zakarun Turai data gabata.
Ana dai ganin azabar da dan wasan ya ganawa Liverpool din ne yayin waccen haduwa ya sanya ta kwallafa rai akansa.
Dama dai tun awancen lokaci anjiyo mai horas da Liverpool Jogen Klub na yabawa dan wasan, yana mai bayyana shi da dan wasa mai karfi da sauri da kuma dabarar zura kwallo a raga.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu