Isa ga babban shafi

La Liga ta zargi shugaban PSG da raina mutane

Shugaban hukumar babbar gasar kwallon kafar Spain Javier Tebas ya zargi shugaban kungiyar PSG Nasser Al-Kheleifi da shirga karya ba tare da ko jin kunya ba, da kuma zama mai girman, bayan da Al-Kheleifin ya kare matakin da ya dauka na kashe makudan kudade,  domin hana dan wasansa Kylian Mbappe kulla yarjejeniya da Real Madrid.

Shugaban gasar La Liga Javier Tebas.
Shugaban gasar La Liga Javier Tebas. AFP/Archivos
Talla

A cikin wata ganawa da yayi a da fitacciyar Jaridar nan ta Marca da ake wallafawa a birnin Madrid, shugaban na  PSG ke cewa su na aiwatar da dukkanin abinda suka gad ama ne domin suna da yakinin za su iya hakan.

Al-Kheleifi ya kara da cewa ba tsarinsa bane tattaunawa akan wasu kungiyoyi ko batutuwan da suka shafi wasannin kwallon kafar wasu nahiyoyi, zalika ba sa yi wa kowa katsalandan a harkokinsa, dan haka su ma ba za su bari a yi musu hakan ba.

Jim kadan bayan watsa hirar, shugaban La Liga, Tebas, ta shafinsa na twitter ya caccaki shugaban na PSG da cewar mayar da sauran takwarorinsa da kuma sauran masu ruwa da tsaki a fagen kwallon kafa wawayen da basu san ma abinda suke yi ba, baya ga tsabar girman kan da yake nunawa.

A makon da ya gabata ne dai, hukumar gasar La Liga ta shigar da karar kungiyoyin PSG da Manchester City, bisa tuhumarsu da karya dokar kashe kudade wajen sayen ‘yan wasa ko biyansu albashi fiye da kudaden da suke samu, wato dokar ‘Financial Fair Play’ a turance.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.