Isa ga babban shafi

Gareth Bale zai koma Los Angeles FC ta Amurka

Gareth Bale na Real Madrid ya cimma yarjejeniya da kungiyar kwallon kafa ta Los Angeles FC da ke doka gasar MLS a Amurka a wani farashi da ba a kai ga bayyanawa ba.

Gareth Bale yayin karawar Wales da Switzerland.
Gareth Bale yayin karawar Wales da Switzerland. AP - Ozan Kose
Talla

Bale mai shekaru 32 wanda shi ne Kyaftin din tawagar kasarsa Wales ya kai ga kulla yarjejeniyar ne bayan karewar kwantiraginsa da Real Madrid wato dai ya kulla sabuwar yarjejeniyar ne a kyauta.

Bale wanda ya lashe kofin zakarun Turai sau 5 a baya an rika alakanta shi da komawa Tottenham ko kuma Cardiff City da ke mahaifarsa.

Har zuwa yanzu dai Los Angeles FC ba ta kai ga sanar da kulla yarjejeniyar ba, sai dai Gareth Bale ya wallafa a shafinsa na Twitter tun a karshen mako cewa zai hadu da magoya bayansa a Los Angeles nan ba da jimawa ba.

A shekarar 2013 ne Barcelona ta sayo Bale kan farashin fam miliyan 85 matsayin dan wasa mafi tsada a wancan lokaci kuma ya bata muhimmiyar gudunmawa a tsawon lokacin da ya shafe yana taka mata leda.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.