Isa ga babban shafi

Galadima ya karbi ragamar shugabancin kungiyar Kano Pillars

Gwamnan Kano Abdullahi Umar ya maye gurbin Surajo Yahya da Ibrahim Galadima a matsayin shugaban kungiyar Kano Pillars, wanda kuma a yanzu haka shi ne shugaban hukumar kula da wasanni a jihar ta Kano.

Tsohon Shugaban Hukumar NFA, Alhaji Ibrahim Galadima (Na biyu daga bangaren hagu) a lokacin da yake jawabi ga ‘yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars a filin wasa na Sani Abacha dake Kano.
Tsohon Shugaban Hukumar NFA, Alhaji Ibrahim Galadima (Na biyu daga bangaren hagu) a lokacin da yake jawabi ga ‘yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars a filin wasa na Sani Abacha dake Kano. © Daily Trust
Talla

Tsohon shugaban Kano Pillars ya rasa matsayinsa ne, bayan da a makon jiya hukumar kula shirya gasar Firimiyar Najeriya LMC ta kore shi daga gasar ta kwararru, saboda cin zarafin mai taimakawa alkalin wasa da yayi, Olalekan Daramola, a lokacin da kungiyar Dakkada FC daga jihar Akwa Ibom suka farke kwallo 1-1, yayin karawar da suka yi da Pillars a Kano.

Sai dai cikin sanrwar da gwamnatin Kano ta fitar dangane da sabon nadin da ta yi, ta ce Ibrahim Galadima ya karbi shugabancin kungiyar Pillars ne a matsayin rikon kwarya, zalika sanarwar ba ta ce komai ba dangane da cin zarafin alkalin wasan da tsohon shugaban kungiyar yayi a makon jiya.

Baya ga ladabtar da Surajo Yahya dai, hukumar ta LMC ta laftawa kungiyar Kano Pillars biyan tarar naira miliyan 2 da miliyan 700.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.