Isa ga babban shafi

Christian Eriksen na duba yiwuwar amsa tayin Manchester United

Dan wasan gaba na Denmark Christian Eriksen ya amince da tayin da Manchester United ta yi masa wanda zai kai shi ga kulla yarejejeniya da kungiyar cikin wannan kaka.

Dan wasan gaba na Denmark Christian Eriksen.
Dan wasan gaba na Denmark Christian Eriksen. AP - Wolfgang Rattay
Talla

Eriksen mai shekaru 30 wanda kwantiraginsa ya kare da Brentford a watan jiya, Manchester United na da damar sayenshi a kyauta.

Dama dai dan wasan ya sanya hannu ne kan gajeruwar yarjejeniya da Brentford a bara, a wani yanayi da ba a yi tsammanin dan wasan ya bayar da gagarumar gudunmawa ba, musamman la’akari da jinyar da ya yi, wadda ta kai ga yi masa dashen na’urar taimakawa zuciya.

Manajan Brentford Thomas Frank na da kwarin gwiwar Eriksen ya amince da sanya hannu kan sabon kwantiragi da kungiyar, sai dai tagomashin da ke tattare da yarjejeniyar shekaru 3 da Manchester United ta yi masa tayi ka iya sauya tunanin dan wasan.

Idan har Eriksen ya amince da kulla kwantiragin da Manchester United, kenan zai zama kari kan ‘yan wasa irinsu Tyrell Malacia da kungiyar ta saya a baya-bayan nan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.