Isa ga babban shafi

EURO 2022: Wasu manyan 'yan siyasar Birtaniya za su shiryawa tawagar mata liyafa

Masu fafutukar zama fira ministan Birtaniya biyu, sun sha alwashin daukar nauyin gudanar da liyafa, domin karrama tawagar kwallon kafar matan kasar da suka samu nasarar lashe gasar mata ta nahiyar Turai a ranar Lahadi.

Karon farko a tarihi da kungiyar kwallon kafa ta ma ta lashe gasar ta EURO a Ingila.
Karon farko a tarihi da kungiyar kwallon kafa ta ma ta lashe gasar ta EURO a Ingila. REUTERS - LISI NIESNER
Talla

Fara minista Boris Johnson na fuskantar suka kan zargin da ake yi masa na kin karrama ‘yan wasan.

Tawagar matan dai ta lashe gasar Euro 2022 a filin wasa na Wembley da ke Landan, wacce ta kasance babbar nasara da tawagar ta taba samu a karon farko a tarihin Ingila tun shekarar 1966.

Mista Johnson bai samu halartar wasan karshen da aka yi ba, sannan kuma bai halarci bude wasan guje-guje da tsalle-tsalle na kungiyar kasashen renon Ingila wato Commonwealth a makon da ya gabata a Birmingham ba.

Sakatariyar harkokin wajen kasar Liz Truss wacce ta halarci wasan karshe na ranar Lahadi da kuma tsohon ministan kudi Rishi Sunak sun ce ya zama wajibi tunda suka kai ga gaci, su shiyrawa tawagar matan liyafar a fadar Downing.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.