Isa ga babban shafi

Ronaldo da Maguire na shan zagi a dandalin Twitter a cewar wani rahoto

Wani bincike da aka gudanar a Birtaniya ya bayyana cewar fitattun Yan wasan Manchester United guda biyu, wato Chrstiano Ronaldo da Harry Maguire aka fi zagi a dandalin twitter.

Christiano Ranaldo dai na fatan Manchester United za ta sanya shi a kasuwa domin samun damar sauya sheka
Christiano Ranaldo dai na fatan Manchester United za ta sanya shi a kasuwa domin samun damar sauya sheka © Marca
Talla

Rahotan da hukumar dake kula da kafofin sada zumuntar kasar ta gudanar da ake kira Ofcom ya ce daga cikin sakonni miliyan 2 da dubu 300 da aka aike a zagaye na farko na gasar Firimiya a kakar da ta gabata, kusan 60,000 duk zagi ne da aka yiwa 7 daga cikin manyan 'yan wasa 10 da suke kasar.

Sakamakon binciken yace rabin wadannan sakonni an aikewa 'yan wasa 12, kuma 8 daga cikin su sun fito ne daga Manchester United.

Ofcom ta ce ta zabi twitter ne wajen gudanar da binciken saboda shine yafi farin jini ga 'yan wasan da kuma saukin samun bayanan da ake bukata domin yin binciken.

Hukumar tace tana shirin samar da wata fasaha wadda zata kare masu amfani da irin wadannan kafofi daga batunci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.