Isa ga babban shafi

Hukumar kwallon kafar Afrika za ta kaddamar da gasar Super League

Shugaban hukumar kwallon kafar Afrika Patrice Motsepe zai kaddamar da gasar Super League ta kungiyoyin kwallon kafar Afrika, tare da alkwarin dala miliyan dari ga kungiyoyin nahiyar.

Shugaban hukumar kwallon kafar Afrika Patrice Motsepe.
Shugaban hukumar kwallon kafar Afrika Patrice Motsepe. © Fadel Senna/AFP
Talla

Tun da shugaban hukumar kwallo kafar duniya, FIFA Gianni Infantino ya bada shawarar gasar a farkon shekarar 2020 ne ake ta shiri tare da kokakrin tsara gasar, kuma babu irin turjiyar da makamancin wannan yunkuri ya gamu da shi a Turai cikin shekarar da ta gabata.

Kungiyar ‘yan wasa a Afrika ta Kudu ce kawai ta soki wanna shiri a wata sanarwa da ta fitar a wannan mako, inda ta ce wannan gasa, idan aka fara ta, za ta yi mummunan tasiri a kan kwallon kafar kwararru a Afrika ta Kudu.

Motsepe ya yi ikirarin cewa idan har aka fara wannan gasar ta Super League, za ta bai wa kungiyoyi damar biyan manyan ‘yan wasa albashi dai dai da yadda ake biyan na Turai, lamarin da zai sa su rage dokin ketarawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.