Isa ga babban shafi

FA ta aikewa Conte da Tuchel takaddar tuhuma kan rikicinsu a filin wasa

Hukumar kwallon kafar Ingila ta rubuta takardun tuhuma ga Thomas Tuchel da Antonio Conte, wato masu horas da kungiyoyin Chelsea da Tottenham, biyo bayan rikicin da suka yi da ya kai ga kusan bai wa hammata iska a tsakani.

Mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Chelsea Thomas Tuchel.
Mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Chelsea Thomas Tuchel. AP - Neil Hall
Talla

Rikicin masu horaswar ya auku ne a yayin wasan da aka tashi 2-2 tsakanin Tottenham da Chelsea a ranar lahadin da ta gabata, inda hatta a bayan kammala wasan sai da aka sake cacar baka tsakanin manajojin, abinda ya sanya alkalin wasa baiwa kowannensu jan kati.

A halin yanzu hukumar kwallon kafar Ingila FA ta bai wa Tuchel da Conte nan da zuwa ranar Alhamis, 18 ga watan Agusta don amsa tuhumar da take musu na aikata abin kunyar neman dambacewa da juna a gaban ‘yan kallo.

Daga cikin tuhume-tuhumen da hukumar FA ta gabatar dai, akwai kalaman da Tuchel ya yi bayan wasan game da alkalin wasa Anthony Taylor, Inda Bajamushen ya ba da shawarar kada a sake baiwa Taylor damar alkalancin wasannin Chelsea nan gaba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.