Isa ga babban shafi

Mourinho ya bukaci 'yan wasansa su rika faduwa da gangan saboda fanareti

Kocin AS Roma, Jose Mourinho, ya shaida wa 'yan wasansa cewar daga yanzu su rika yawaita faduwa ko da kuwa da gangan ne, don samun karin damarmakin bugun daga kai sai mai tsaron raga, wato fanareti.

Kocin AS Roma José Mourinho.
Kocin AS Roma José Mourinho. REUTERS/Dylan Martinez
Talla

A ranar Lahadin da ta gabata, Mourinho ya yi fuskatar da ta kusan kai shi ga rafke alkalin wasa Daniele Chiffi, saboda hana su damar bugun fanareti, a wasan da Atalanta ta doke su da 1-0.

yayin tankiyar sai dai aka rike Mourinho domin hana shi make alkalin wasan, saboda watsin da yayi da kiran ya hukunta dan wasan Atalanta Caleb Okoli da ya yi wa Nicolo Zaniolo keta, abinda ya sanya jami’in ya kori kocin daga fili bayan daga masa jan kati.

A lokacin da yake raddi kan abinda ya faru ne kuma Mourinho ya ce da dan wasansa Zanioli bai yi kokarin mikewa tsaye ba, a lokacin da aka yi masa keta, to da sun samu damar bugun faneretin da suka cancanci a basu.

Yanzu haka AS Roma tana matsayi na shida a kan teburin Seria A, da maki 13 bayan buga wasanni bakwai na farko.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.