Isa ga babban shafi

Ingila ta shiga rukunin 'yan dagaji a gasar kasashen Turai

Kocin Ingila, Gareth Southgate ya ce jagorancin babbar tawagar kwallon kafar Ingila wani babban kalubale ne a wannan lokaci mai cike da sarkakiya, kuma ya ce akwai bukatar jajircewa a tattare da ‘yan wasan tawagar.

Kocin tawagar kwallon kafar kasar Ingila kenan, Gareth Southgate
Kocin tawagar kwallon kafar kasar Ingila kenan, Gareth Southgate AFP
Talla

Ingila sun samu koma baya zuwa rukunin ‘yan dagaji a gasar kasashen Turai ta Nations League, bayan da Italiya suka lallasa su da ci 1 mai ban haushi ranar Juma’a a birnin Milan.

Za su fafata da Jamus a ranar Litinin din nan, bayan da suka buga wasanni har 5 ba tare da nasara ba a karon farko tun shekarar 2014.

Southgate ya ce haka lamarin yake wani lokaci, kuma ba shi ne koci na farko da ya taba jagoranatar tawagar a lokaci mai cike da jarawaba irin wannan ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.